Taron ya fara gudana ne da buɗewa da karatun Alqur'ani Mai Girma, sai IM Production suka yi Tamsiliyya Mai taken 'Ranar Ghadeer-khum'. Tamsiliyya ta isar da sako sosai akan abinda ya shafi Miƙa wulaya Manzon Allah (SAWW) ga al'ummarsa.
Wakilin Yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (H) na garin Shado, Malam Abdulmumin Abubakar ya gabatar da Jawabi a Taron.
A karshe mawaƙa sun yi wakokin murna da ranar Ghadeer-khum, sai aka yi Addu'a aka tashi.
An fara lafiya an kammala lafiya.
Daga Ammar .A. Shado
Zaria Media Forum
Your Comment